Majalisar UN ba ta jin dadin abubuwan da ke faruwa a Gwamnatin Buhari

Majalisar UN ba ta jin dadin abubuwan da ke faruwa a Gwamnatin Buhari

Da alamu dai Majalisar dinkin Duniya ba ta jin dadin abubuwan da su ke faruwa a halin yanzu a Najeriya musamman a bangaren sha’anin tsaro da kuma harkar zabe da matsin tattalin arziki inji Jaridar Vanguard.

Majalisar UN ba ta jin dadin abubuwan da ke faruwa a Gwamnatin Buhari

An fara kokawa da halin da Najeriya ta ke ciki a UN

Majalisar tsaro ta UN ta nuna damuwa game da matsalolin da ake samu wajen harkar zabe da kuma halin ka-ka-ni-ka-yi da mutanen Najeriya su ke ciki. Har wa yau dai UN ta nuna rashin jin adi kan rashin tsaro da rikicin Makiyaya a Kasar.

Majalisar inkin Duniyar ta fitar da jawabi ne jiya bayan yunkurin da Jami’an tsaro su kayi na kokarin zagaye harabar Majalisar Kasar kwanaki. An soki wannan danyen aiki wanda har ta ja aka tsige Shugaban DSS na kasar Lawal Daura.

KU KARANTA: 'Yan kunar bakin wake sun kashe wasu mutane a Adamawa

UN tayi tir da abin da yake faruwa na hare-haren ‘Yan ta’adda da sauran su inda ta bada shawarar yadda za a gyara halin da ake ciki a kasar. Majalisar ta Duniya tace barnar da ‘Yan ta’adda ke yi a yankin tafkin Chad yana maida kasar baya kwarai da gaske.

Majalisar tsaron ta UN mai mutum 15 ta kuma nemi ayi kokarin kawo karshen rikicin da ake samu tsakanin Makiyaya da Manoma a wasu sashen na kasar. UN ta kuma nemi ayi maganin ‘Yan Boko Haram da ke amfani da yara wajen kunar bakin-wake.

Takkadamar da ta faru a Majalisa a makon jiya ta sa an fara zargin Gwamnati da kokarin yi wa tsarin mulkin Najeriya hawan kawara. Bayan nan kuma dai ana fama da matsi na tattalin arziki a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel