EFCC ta mayar da martini game zargin hannunta cikin bahallatsar Majalisa

EFCC ta mayar da martini game zargin hannunta cikin bahallatsar Majalisa

- Rubutun wani hadimin Buhari a Jarida ya harzuka hukumar EFCC

- Ta kasa daurewa har sai da ta mayar da martani

Hukumar hana cin hanci da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta mayar da martini ga mashawarcin shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin siyasa Babafemi Ojudu, cewa ba ta da wata alaka da shugaban majalisar dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki.

EFCC ta mayar da martini game zargin hannunta cikin bahallatsar Majalisa

EFCC ta mayar da martini game zargin hannunta cikin bahallatsar Majalisa

Ojudu ya dai yi zargin cewa EFCC nada wata alaka da abubuwan da suke faruwa majalisar dattijai cikin wani rubutu da ya yi.

Wanda batun mamayar da jami’an tsaron suka yiwa majalisar kasar nan ya fantsama aka rika bayyana mabambantan ra’ayi akansa cikin makon da ya gabata, inda hadimin Buharin ya shiga cikin sahun masu cewa hukumar EFCC na aiki tare da Saraki domin yi wa dimukuradiyya tare da gwamnatin shugaba Buhari zagon-kasa.

KU KARANTA: Idon EFCC ya hango wasu makudan kudaden jihar Akwa Ibom a asusunsu wasu lauyoyi

Sai dai shugaban majalisar Bukola Saraki ya fito ya karyata haka, har ya kara da cewa wanda ya fadi hakan to ya raina wa ‘yan Najeriya hankali.

Ita ma hukumar EFCC ta bakin kakakin ta Wilson Awujeren, ta ce zargin da Ujudu ya yi a matsayinsa na mashawarcin shugaban kasa ba gaskiya ba ne, kuma abin takaici da mamaki ne.

Ya kara da cewa ya kamata jama’a su yi watsi da maganar Ujudu, tare da yin kira ga ‘yan siyasa su rika tuntuba suna tantance batutuwa kafin su kai alkalaminsu kan takarda, ko kuma kafin su yi wani furucin da bai dace ba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel