Gwamnan Enugu yana damawa da Matasa masu jini-a-jika a Gwamnatin sa

Gwamnan Enugu yana damawa da Matasa masu jini-a-jika a Gwamnatin sa

Gwamnan Jihar Enugu ya bayyana cewa sama da matasa 1000 na Jihar ke rike da mukamai a wannan Gwamnati. Gwamnatin Jihar na kokarin samawa Matasa aikin yi ne domin maganin zaman-banza.

Gwamnan Enugu yana damawa da Matasa masu jini-a-jika a Gwamnatin sa

Gwamna Uguwanyi yana damawa da danyun Matasa a Jihar Enugu

Gwamnatin Jihar Enugu na kokarin ganin yadda za ta rage masu zaune-gari-banza don haka ta samawa Matasa da dama aiki a matakai daban-dabam na Gwamnati. Kwamshinan Matasa na Jihar Joseph Udedi ya bayyana wannan jiya.

Mista Joseph Udedi ya bayyana cewa kwanan nan ne Gwamnan ya nada wani kwamiti karkashin Mataimakiyar sa Cecilia Ezeilo domin duba manyan kamfanonin Gwamnati da su ka gaza da za a saidawa ‘Yan kasuwa su tada su.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun nemi su yi bore a fagen fama

Idan har ‘Yan kasuwa su ka saye wadannan kamfanoni, za a babbako da su wanda zai yi sanadiyyar samun aikin mutane da dama. Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Gwamnan ya nada Matasa kusan 600 cikin masu ba sa shawara.

Har wa yau mutum 10 cikin 24 da ke Majalisar dokokin Jihar ta Enugu Matasa ne shakaf. Samda kashi 70% na Kamsilolin Jihar kuma dai Matasa ne. Bari ma ta wannan, akwai Ma’aikatan titi duk Matasa fiye da 1000 da aka dauka aiki.

Kwamishinan na Matasa na Jihar ya kuma bayyana cewa akwai Matasa fiye da 3000 na Jihar da Gwamnatin Tarayya ta ke horaswa ta tsarin nan na ITF. Gwamnatin Ugwanyi ta kuma ta biyawa Matasa kusan 1000 kudin Makaranta a Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel