Yan kunar bakin wake sun sabbaba mutuwar mutane 10 a Madagali

Yan kunar bakin wake sun sabbaba mutuwar mutane 10 a Madagali

Akalla mutane goma ne suka rigamu gidan gaskiya bayan wani harin kunar bakin wake da wasu mata guda biyu suka kai a wani wuri mai tarin jama’a a cikin karamar hukumar Madagali na jihar Adamawa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan hari ya faru ne a ranar Asabar, 11 ga watan Agusta, inda wasu Mata biyu dauke da da kayan bama bamai suka tayar da kansa a hanyar shiga garin Madagali ta yankin dake makwabtaka da garin Gwoza na jihar Borno.

KU KARANTA: Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

Wani mazaunin yankin mai suna Aura Garga ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace da misalin karfe 12 na ranar Asabar yan kunar bakin waken suka kai hari, harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsu da wasu mutane goma.

Sai da Garga yace: “Da dama daga cikin wadanda suka samu rauni a sakamakon harin an garzaya dasu zuwa asibitoci daban daban don samun lafiya."

Duk kokarin da majiyarmu ta yi don jin ta bakin hukumomin soji dake jibge a garin Mubi ya gagara, amma dama garin Madagali dake kimanin nisan kilomita 250 daga garin Yola ya sha fuskantar hare haren Boko Haram, har bayan shekarar 2015 da Sojoji suka kwato garin daga hannun Boko Haram.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel