Ina taya Oyegun murnar cika shekaru 79 a Duniya – Buhari

Ina taya Oyegun murnar cika shekaru 79 a Duniya – Buhari

Mun samu labari daga fadar Shugaban kasa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Cif John Odigie Oyegun murnar zagayowar ranar haihuwar sa a Duniya.

Ina taya Oyegun murnar cika shekaru 79 a Duniya – Buhari

Buhari ya taya Oyegun murnar cika shekara 79 a Duniya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda yanzu haka yana Kasar Landan inda yake hutawa ya taya John Odigie Oyegun wanda ya shugabanci Jam’iyyar APC mai mulki har zuwa kwanakin baya murnar wannan muhimiyyar rana a jiya.

Muhammadu Buhari ya taya John Oyegun murnar cika shekara 79 a Duniya inda yayi masa addu'a Allah ya kara masa lafiya. Shugaba Buhari ya yabi Shugaban APC da aka fara zaba a karon farko a tarihi wanda yace da su aka yi sauyi a Najeriya.

Mun samu labarin nan ne ta daya daga cikin Hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Ranar Lahadi. Bashir Ahmad wanda ke ba Shugaban kasa shawara a kan kafafen yada labarai na zamani ya bayyana wannan a shafin sa na Tuwita.

KU KARANTA: 2019: Atiku Abubakar yayi wa ‘Yan Najeriya wani babban alkawari

Tsohon Shugaban na Jam’iyyar APC na kasa baki daya ya cika shekaru 79 da haihuwa a ban kasa a Ranar 12 ga watan Agustan nan. A watan jiya ne Odigie-Oyegun ya sauka daga kujerar sa na Shugaban Jam’iyya aka nada Adams Oshimohole.

An haifi John Odigie-Oyegun ne a shekarar 1939 kuma yayi Gwamnan Jihar sa ta Edo na wani ‘dan lokaci a shekarar 1983 kafin Janar Muhammadu Buhari ya hambarar da Gwamnati a lokacin mulkin Soja. A 2014 ya zama Shugaban Jam’iyyar APC.

Jiya kun ji cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki a zaben Sanatan Yankin Arewacin Katsina watau Honarabul Ahmad Babba-Kaita ya lashe zaben Majalisar Dattawan da aka yi a Ranar Asabar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel