Bayan kisan mijin ta, Maryam Sanda ta haifi zankadeden saurayi

Bayan kisan mijin ta, Maryam Sanda ta haifi zankadeden saurayi

Matar nan da labarin ta ya zagaye gari wadda ake zargin ta kashe mijin ta a watannin baya mai suna Maryam Sanda dake zaman ta a garin Abuja yanzu haka dai ta haifi zankadeden saurayi.

Majiyar mu ta gidan jaridar Sahara Reporters dai ta bayyana cewa ta samu zarafin bankado labarin haihuwar tata ne duk kuwa da irin boyon da iyalan ke yi don kar labarin ya fita.

Bayan kisan mijin ta, Maryam Sanda ta haifi zankadeden saurayi

Bayan kisan mijin ta, Maryam Sanda ta haifi zankadeden saurayi

KU KARANTA: Soyayyar Rahma Sadau da wani jarumi ta fara fitowa fili

Legit.ng ta samu cewa Maryam Sanda ta haihu ne a ranar Talatar da ta gabata kuma tuni har shire-shiren yin bikin sunan jaririn ya yi nisa a ranar Talata mai zuwa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Maryam wadda yanzu haka ke fuskantar shari'ar zargin kisan mijin ta an bayar da ita beli ne sakamakon cikin da ke gareta.

A wani labarin kuma, da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa an ga gawar daya daga cikin hadiman Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano kuma mai taimaka masa na musamman mai suna Mista Randie Chima a dakin sa.

Majiyar ta mu dai ta tabbatar mana da cewa a ranar Juma'a hadimin gwaman yayi ta hidimar sa lafiya lau kuma har ma yaje wani wurin shagali da daren juma'ar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel