Da dumin sa: Hadimin wani gwamna a Najeriya ya hade rai ya mutu a dakin sa

Da dumin sa: Hadimin wani gwamna a Najeriya ya hade rai ya mutu a dakin sa

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa an ga gawar daya daga cikin hadiman Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano kuma mai taimaka masa na musamman mai suna Mista Randie Chima a dakin sa.

Majiyar ta mu dai ta tabbatar mana da cewa a ranar Juma'a hadimin gwaman yayi ta hidimar sa lafiya lau kuma har ma yaje wani wurin shagali da daren juma'ar.

Da dumin sa: Hadimin wani gwamna a Najeriya ya hade rai ya mutu a dakin sa

Da dumin sa: Hadimin wani gwamna a Najeriya ya hade rai ya mutu a dakin sa

KU KARANTA: An gano abun da ya hana Yakubu Dogara barin APC

Legit.ng ta samu cewa 'yan sandan jihar dai sun tabbatar da aukuwar lamarin sannan kuma sun ce tuni har sun fara bincike domin gano musabbabin dalilin mutuwar ta sa.

A wani labarin kuma, Matar nan da labarin ta ya zagaye gari wadda ake zargin ta kashe mijin ta a watannin baya mai suna Maryam Sanda dake zaman ta a garin Abuja yanzu haka dai ta haifi zankadeden saurayi.

Majiyar mu ta gidan jaridar Sahara Reporters dai ta bayyana cewa ta samu zarafin bankado labarin haihuwar tata ne duk kuwa da irin boyon da iyalan ke yi don kar labarin ya fita.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel