Abin kunya: Kyauta Obasanjo yake bawa mata rijiyar man fetur bayan yin lalata da su – Farfesa Soyinka

Abin kunya: Kyauta Obasanjo yake bawa mata rijiyar man fetur bayan yin lalata da su – Farfesa Soyinka

Mashahurin malamin boko mai lambar girma ta Farfesa, Wole Soyinka, ya kalubalanci tsohon shugaban kasa Obasanjo da ya rantse bai taba bayar da kyautar rijiyar man fetur ga mace ba bayan biyan bukatarsa da ita ba.

Farfesa Soyinka ya yi wannan furuci ne a Legas yayin cigaba da gabatar da wasu jerin rubuce-rubuce da ya yi a kan tsohon dan gwagwarmaya kuma fitaccen lauya, Gani Fawehimi.

Soyinka ya bayyana cewar Obasanjo ya sani sarai cewar ba ya zargin mutum a kan duk wata Magana da ba ta da tushe balle makama.

Ina mai kalubalantar Obasanjo da ya fito fili, tsakaninsa da ‘yan Najeriya, ya musanta cewar bai taba bayar da kyautar rijiyar man fetur ga mata ba bayan kwanciya da su,” a cewar Soyinka.

Abin kunya: Kyauta Obasanjo yake bawa mata rijiyar man fetur bayan yin lalata da su – Farfesa Soyinka

Farfesa Wole Soyinka

Bana zargin mutum a kan duk wata jita-jita maras tushe. Ko ku da kan ku kun san hakan. Ba na munafurci kuma ba neman mulki nake yi ba balle na bata sunan wani ba don samun daukaka. Ina fadar gaskiya ne domin ‘yan Najeriya su san shugabannin dake kaunar su da kuma makiyansu,” in ji Soyinka.

DUWA WANNAN: PDP ta kayar da APC a zaben mayen gurbi, ta lashe kujerar majalisa

Soyinka ya kafa hujja da wata wasika da tsohon gwamna a mulkin soji, Abubakar Umar, ya taba aikewa Obasanjo inda yake zarginsa da bayar da rijiyar man fetur ta haramtacciyar hanya da ta saba da doka.

Kazalika Soyinka ya bayyana yadda Obasanjo ke amfani da wasu kwararrun masu kisa domin kawar da abokan adawarsa na siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel