Mummunar musayar wuta da ‘yan bindiga, ‘yan sanda 4 sun rasu a Kaduna

Mummunar musayar wuta da ‘yan bindiga, ‘yan sanda 4 sun rasu a Kaduna

- 'Yan bindiga na cigaba da kaiwa jami'an 'yan sanda hari a Najeriya

- A Kaduna, wasu da ake zaton 'yan bindiga ne sun kashe jami'an 'yan sanda hudu

- Kwanakin baya ma a birnin tarayya wasu 'yan bindigar suka harbe jami'an 'yan sanda 7 tare da yin awon gaba da bindigunsu

Kwanan wasu ‘yan sanda hudu da suke kan hanyarsu ta zuwa sintiri ya kare a wata zazzafar musayar wutar da suka yi da wasu wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne a kauyen Jankasa dake yankin Rigasa na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Mummunar musayar wuta da ‘yan bindiga, ‘yan sanda 4 sun rasu a Kaduna

Mummunar musayar wuta da ‘yan bindiga, ‘yan sanda 4 sun rasu a Kaduna

Jami'an ‘yan sandan sun hadu da ajalinsu da misalin karfe bakwai na yammacin jiya Asabar a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa sintiri.

Jim kadan da yin kicibis din nasu ne suka fara musayar wuta a tsakaninsu da barayin wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan ‘yan sandan guda hudu.

KU KARANTA: Rikicin Taraba: An kashe mutane 4 tare da raunata wasu 8

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce “Da misalin karfe bakwai na yammacin ranar Asabar ne, jami'an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna, suka yi musayar wuta tsakaninsu da wasu barayi a kauyen Jankasa dake yankin Rigasa a karamar hukumar Igabi, wanda hakan ya zama silar rasa rayukan jami’ai hudu"

Sai dai har ya zuwa yanzu dai babu rahoton kamo wadannan barayin da suka tafka wannan aika-aika duk kuwa da cewa an aike da karin dakaru domin bin sahu.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel