Guguwar sauyin sheka: Tsohon gwamna a Arewa ya fice daga jam'iyyar APC

Guguwar sauyin sheka: Tsohon gwamna a Arewa ya fice daga jam'iyyar APC

Tsohon mukaddashin gwamna a jihar Adamawa dake a arewacin Najeriya kuma na hannun gwamnan jihar Umaru Jibrilla mai suna Ambasada James Barka ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake tabbatar da ficewar tasa daga jam'iyyar, Mista Barka ya bayar da dalilai na rashin kyautawar gwamnan jihar da kuma rashin gaskiyar da ake tafkawa a gwamnatin a matsayin musabbabin ficewar ta sa.

Guguwar sauyin sheka: Tsohon gwamna a Arewa ya fice daga jam'iyyar APC

Guguwar sauyin sheka: Tsohon gwamna a Arewa ya fice daga jam'iyyar APC

KU KARANTA: Yadda budurwa ta yanke azzakarin saurayin ta a Jigawa

Legit.ng ta samu cewa shidai Mista Barka tsohon Ambasada ne na Najeriya a kasar Malaysia kuma mamba ne a kwamitin shugaban kasa na farfado da yankin arewa ta gabas.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Benue dake a arewacin Najeriya ya bukaci shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole da ya fito bainar jama'a ya bashi hakuri tare da neman gafarar sa game da kazafin da yayi masa a cikin kwanaki bakwai ko kuma ya kai shi kotu.

Gwamna Ortom dai yayi wannan kiran ne ga shugaban jam'iyyar ta hanyar wata takarda da lauyoyin sa suka rubuta, suka kuma rabawa manema labarai a ranar 6 ga watan Agusta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel