Sanatocin APC na neman karawa Bukola Saraki ciwon kai a Majalisa

Sanatocin APC na neman karawa Bukola Saraki ciwon kai a Majalisa

Mun samu labari cewa ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Jihar Delta ta Tsakiya a Majalisar Dattawa watau Sanata Ovie Omo-Agege yayi hira da Jaridar Punch inda ya rantse cewa sai sun tsige Bukola Saraki idan har bai bar kujeran sa ba.

Sanatocin APC na neman karawa Bukola Saraki ciwon kai a Majalisa

Sanata ya sha alwashin sauke Bukola Saraki daga mukamin sa

Sanatan na APC Ovie Omo-Agege ya bayyana cewa natsayar su ita ce Bukola Saraki ya sauka daga matsayin sa na Shugaban Majalisar Dattawa tun da har ya fice daga Jam’iyyar APC wanda ita ce da mulki da rinjaye a Kasar.

Ovie Omo-Agege yace sun nemi Bukola Saraki yayi murabus tun da girma da arziki ko kuma su tsige sa. Sanatan na Jihar Delta yace abin da su ke so shi ne Saraki ya bar matsayin nan na sa ba wai ya bar Majalisa gaba daya ba.

KU KARANTA: Karyar ku ta sha karya: Saraki ya maidawa Jam’iyyar APC martani

Sanatan na Kudancin Kasar ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa tun da har Saraki ya koma Jam’iyyar PDP, babu dalilin da zai sa ya cigaba da shugabantar Majalisar Tarayyar a wannan Gwamnati ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

‘Dan Majalisar ya kuma bayyana cewa su na da duk adadin Sanatocin da ake nema su tsige Bukola Saraki. Kwanaki dai wasu Sanatocin Jam’iyyun adawa su ka tabbatar da mubaya’ar su ga Saraki amma Agege yana ganin duk a banza.

Dazu kun ji labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta kama hanyar lashe zaben wasu ‘Yan Majalisu da aka yi a Arewa Jihohin Bauchi da kuma Katsina da ma Jihar Kogi. Hakan dai na nufin APC na cigaba da kara samun rinjaye a Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel