An rasa rayuka wajen zaben ‘Dan Majalisa a Jihar Kogi

An rasa rayuka wajen zaben ‘Dan Majalisa a Jihar Kogi

Mun samu labari cewa an kashe wani Matashi mai suna Yadou Umoru da yayi yunkurin sace akwatin zabe a Unguwar Pawa a cikin Jihar Kogi. A jiya Asabar ne aka gudanar da zaben ‘Dan Majalisar Tarayya da zai wakilaci Yankin Kogi-Koto-Karfe.

An rasa rayuka wajen zaben ‘Dan Majalisa a Jihar Kogi

Wasu Bayin Allah sun mutu wajen zaben 'Dan Majalisa a Najeriya

Kusan dai mutum 2 su ka sheka lahira a wajen zaben da aka yi a Kogi bayan da aka hallaka wani Bawan Allah da yayi kokarin sace akwatin zaben wata Mazaba a cikin garin Kogi. Wannan mutumi ya mutu ne bayan an bi shi da mugun duka a nan-take.

Ana zargin cewa wanda aka kashe din yaron wanda ke neman takarar kujerar ‘Dan Majalisar ne. Wani wanda aka yi abin a gaban sa ya bayyanawa Jaridar Punch cewa wannan saurayi yayi kokarin sungume akwatin zabe ne sai kuwa aka afka masa.

KU KARANTA: Mutane sun mutu wajen hadarin mota a Jihar Kogi

Jaridar ta nemi ta ji ta bakin Jami’an tsaron da ke Yankin amma abin ya ci tura. Jama’a ne dai su ka dura kan wannan Matashi a gaban gidan Mai Garin Lokoja a Jihar Kogi. Kafin nan dama an kashe wani yayin da shin a yayi yunkurin sace akwati.

Mun ji kishin-kishin din cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar APC ne dai yayi nasara a wannan zabe. Haruna Isah wanda ya samu kuri’u sama da 11, 000 ya doke sauran ‘Yan takarar irin su Injiniya Bashiru Abubakar na Jam’iyyar PDP mai adawa.

Ku na da labari cewa Jam’iyyar APC ta kama hanyar lashe zaben ‘Yan Majalisun da aka yi a Najeriya jiya. Da alamu PDP ta sha kasa a takarar kujerar Sanatan Yankin Daura Mahaifar Shugaba Buhari da kuma Yankin Kudancin Jihar Bauchi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel