Kunci taliyar karshe - PDP ga APGA a Anambra

Kunci taliyar karshe - PDP ga APGA a Anambra

- Gwiwar PDP har yanzu bata sanyaya ba

- Ta bayyana aniyar na kawato jihar anambra daga jam'iyyar APGA

- acewarta dama rigingimun cikin gida ne ya sanya har APGA take tasiri, kuma yanzu duk sun dinke barakar

Jam’aiyyar PDP ta sha alwashin sake kwato jihar Anambra daga wurin jam’iyyar APGA.

Hakan na fitowa ta bakin shugaban kwamitin sulhu na jihar Ngozi Agudozi, a yayin zantawarsa da jaridar PUNCH jiya Asabar.

PDP ta sha alwashin kwato wata jiha a Kudu ko ana ha-maza-ha-mata

PDP ta sha alwashin kwato wata jiha a Kudu ko ana ha-maza-ha-mata

Asali dai Agudozi ya furta hakan ne yayin wani taro da aka gudanar don tunawa da tsohon mataimakin shugaban kasa a jamhuriya ta biyu Dr. Alex Ekwueme, wanda ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kafa jam’iyyar ta PDP.

KU KARANTA: Abubuwa 10 da Saraki ya fada yayin taron Duniya da suka gudanar yau

Anasa jawabin jagoran jam’iyyar a a jihar, Ekwueme Agudosi, ya bayyana cewa daga wannan karon ba zasu sake yarda ayi musu sakiyar da ba ruwa ba.

Jam’iyyar APGA dai ta rinka lashe zabin jihar ne tun daga shekara ta 2006 har kawo wannan 2015.

Agudosi ya jaddada cewa zai sharewa ‘yan jam’iyyar tasu na kasa-kasa hawayensu domin tabbatar da kawo musu sauyi.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel