Wasu Mata sun bayyana soyayyar su tuƙuru ga shugaba Buhari a jihar Bauchi

Wasu Mata sun bayyana soyayyar su tuƙuru ga shugaba Buhari a jihar Bauchi

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito wasu Mata masu kada kuri'u yayin gudanar da zaben maye gurbi a jihar Bauchi, sun kwashi 'yan kallo yayin da suka sumbaci takardun kada kuri'un su tare da karaji da kururuwa ta 'Sai Baba Buhari'.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, wannan lamari ya auku tsakanin wasu Mata hudu yayin kada kuri'un su wurin wani jefa kuri'a dake mazabar Dawaki ta cikin Birnin Bauchin ta Yakubu.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi zargin ko Matan sun yi kuskuren fahimtar wannan zaben na maye gurbin kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu da babban zaben kasa na 2019, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fafata takarar sa.

Wasu Mata sun bayyana soyayyar su tuƙuru ga shugaba Buhari a jihar Bauchi

Wasu Mata sun bayyana soyayyar su tuƙuru ga shugaba Buhari a jihar Bauchi
Source: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, ana amfanin da wannan kalmomin na "Sai Baba" domin bayyana goyon baya ga shugaba Buhari yayin yakin nemen zabe kamar yadda mafi akasarin al'ummar kasar nan suka shahara a kai.

KARANTA KUMA: Kitimurmurar tsige Saraki da Ekweremadu ba za ta yi nasara ba - PDP

Sai da wannan mata kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana sun ki amincewa manema labarai wajen ganawa da su domin tatsar rahoto da bayanai a gare su.

Shugaban hukumar zabe ta wannan reshe, Miss Fai'za Muhammad, ta yabawa mata dangane da cincinrindon da suka yi wajen fitowa domin kada kuri'un su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel