Cinikayya da magudi kawai aka tafka a zaben yau a jihar Kogi

Cinikayya da magudi kawai aka tafka a zaben yau a jihar Kogi

- A wasu wuraren ma kuwa, an ga 'yansandan sun dauke kawunansu ne domin baiwa ja'iran damar su ci karensu babu babbaka

- Zabukan ana yinsu ne na maye gurbin wadanda suka rasu ko barin kujerunsu, a Bauchi, Katsina da Kogi

Cinikayya da magudi kawai aka tafka a zaben yau a jihar Kogi

Cinikayya da magudi kawai aka tafka a zaben yau a jihar Kogi
Source: Depositphotos

Zabukan yau a Lokoja, babban birnin jihar Kogin Kwara, sun zo wa mutane da yadda aka saba gani a jihar, magudi, fada, kwacen kuri'u, dangwale, sare sare da ma dambacewa. Wasu wuraren kuwa ma cinikin kuri'un ake gar-da-gara saye kuri'ar.

DUk da yawan jami'an tsaro da aka jibge a jihar, hakan bai hana 'yan daba da sara suka cin karen su babu babbaka ba.

DUBA WANNAN: Yadda aka yi zabe a Bauchi a yau

A wasu wuraren ma kuwa, an ga 'yansandan sun dauke kawunansu ne domin baiwa ja'iran damar su ci karensu babu babbaka.

Zabukan ana yinsu ne na maye gurbin wadanda suka rasu ko barin kujerunsu, a Bauchi, Katsina da Kogi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel