Kitimurmurar tsige Saraki da Ekweremadu ba za ta yi nasara ba - PDP

Kitimurmurar tsige Saraki da Ekweremadu ba za ta yi nasara ba - PDP

Jam'iyyar adawa ta PDP ta gargadi fadar shugaban kasa da kuma jam'iyyar APC akan su farka daga mafarkin su na tsige shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da kuma mataimakin sa, Ike Ekweremadu.

A yayin danganta wannan lamari da rudu, PDP ta bayyana cewa ya kamata jam'iyyar APC da makarrabanta sun ankara kan cewa ba bu wani tanadi cikin kundin tsari ko dokar kasar nan da zai ba su damar tsige Sanatocin daga mukaman su.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, kakakin jam'iyyar Mista Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana hakan ciki wata sanarwa a ranar Juma'ar da ta gabata da cewar jam'iyyar ta gaza samu wata dabara ko takunkumi na fatattakar Saraki da mataimakin sa.

Kitimurmurar tsige Saraki da Ekweremadu ba za ta yi nasara ba - PDP

Kitimurmurar tsige Saraki da Ekweremadu ba za ta yi nasara ba - PDP

Mista Ologbondiyan ya ci gaba da cewa, ba bu shakka jam'iyyar APC ce ta kulla kitumurmurar mamayar da jami'an tsaro na hukumar DSS suka yiwa farfajiyar majalisar dokoki ta tarayya a ranar Talatar da gabata.

KARANTA KUMA: Mu na alfahari da goyon bayan ka akan 'Dan mu, Buhari - Sarkin Daura ga Osinbajo

Legit.ng ta fahimci cewa, akwai bukatar kaso 2 bisa 3 na adadin Sanatocin majalisar dattawa su zatar da wannan hukunci na tsige Saraki da Mataimakin sa, inda ake bukatar kimanin Sanatoci 73 cikin 109 dake kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan badakala ta kunno kai yayin da shugaban majalisa ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a makon da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel