Rashin tausayi: Injiniya ya boye gawar makwabcinsa da ya taka da mota a kwalbati

Rashin tausayi: Injiniya ya boye gawar makwabcinsa da ya taka da mota a kwalbati

Wani injiniyan komfuta mai suna Samuel ya tsere bayan ya yi sanadiyar rasuwar makwabcinsa mai suna Taiwo Aiyegbusi a unguwar Alagbado da ke Jihar Legas.

Samuel ya kade makwabcinsa da mota ne Ibari Road lokacin da yake hanyarsa na komawa gida misalin karfe 9 na daren Lahadi. Bayan ya bugu shi da mota, ya jefar da gwarsa cikin kwata daga bisani ya tsere daga unguwar.

Punch ta ruwaito cewa Taiwo, wanda makaniken mota ne ya kaiwa abokinsa ziyara ne amma lokacin da ya ke hanyarsa na komawa gida sai mota ta kwubcewa Samuel hakan yasa ya buge shi ya hada jikinsa da Pole wayar wutar lantarki.

Rashin tausayi: Injiniya ya boye gawar makwabcinsa da ya taka da mota a kwalbati

Rashin tausayi: Injiniya ya boye gawar makwabcinsa da ya taka da mota a kwalbati

Majiyar Legit.ng ta gano cewa Samuel yana dawowa daga wajen party ne tare wasu abokansa guda uku a cikin motar lokacin ya buge makwabcinsa.

DUBA WANNAN: An samu barkewar takaddama a Ningxia kan rushe masallaci

An ce Samuel da abokansa sun dauki Taiwo zuwa wani asibiti mai zaman kansa a unguwar amma aka umurci su tafi dashi Taiwo zuwa babban asibitin Ikeja. Sai dai daga baya sun jefa gawarsa a kwata bayan ya mutu a hanyar zuwa asibitin.

Daga baya Samuel ya dawo wajen da hatsarin ya afku ya janye motarsa kuma ya garzaya kasuwar Jankara ya sayarwa 'yan gwangwan motar sannan ya tsere.

Daga baya an gano cewa Samuel bai garzaya da Taiwo asibiti nan take bayan ya buge shi saboda masu gidajen hayar da Pole wayar take sun tsare shi sun bukaci ya biya su N50,000 kudin Pole wayar da ya bata a lokacin Taiwa na kwance a sume.

Wani abokin maraigayin mai suna Inuesokan yace Samuel da Taiwo sun taso a unguwa daya ne kuma sun san juna kafin Taiwo ya canja gida ya koma Malomo Street dake Alagbado. Shi kuma Samuel yana zaune a Odutola Estate duk dai a Alagbado.

Kwamishinan 'yan sandan Legas, CSP Chike Oti, ya tabbatar da afkuwar lamarin yace a yanzu hukumar ta baza jami'anta domin neman Samuel. Ya kara da cewa duk wandanda aka samu da hannu cikin kisar Taiwo da jefa gawarsa a kwata zasu fuskanci hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel