Yadda muka kasa tsayar da Tambawal a cikin APC - shugaban APC Oshiomhole

Yadda muka kasa tsayar da Tambawal a cikin APC - shugaban APC Oshiomhole

- An kasa gane ainahin dalilan da suka sanya Tambawal ya bar APC

- Shi dai ba takura masa gwamnatin Tarayya tayi ba, ba kuma bibiyarsa EFCC tayi ba

- Ga alama ya san me ya taka, ga alama kuma, ya kwapsa ne wa kai nai a 2019

Yadda muka kasa tsayar da Tambawal a cikin APC - shugaban APC Oshiomhole

Yadda muka kasa tsayar da Tambawal a cikin APC - shugaban APC Oshiomhole

A hira da manema labarai, shugaban APC mai mulki, Adams Oshiomhole, ya fayyace dalilin da yasa suka kasa hana Tambawal barin jam'iyyar tasu ta APC.

A cewarsa, duk da bamu so ba, baka sulhu da wanda baya neman sulhu, kuma baka ja da wanda ya sanya babban muradi da buri a gabansa.

Maganar tasa tayi kama ne da shaguben cewa duk wanda yace zai hadiyi gatari, botar ake sakam masa a gani.

Kamar dai Tambawal ya kyalla ido ne yana kallon bbbar kujera lamba daya, ko kuma ita aka yi masa alkawari a jam'iyyar da ya koma mai manyan giaye da kuraye, wadanda suma kujerar ta kai su.

Ko ma dai menene, akwai dirama a watannin nan shidda, domin babu wanda bayyi mamakin sauyin shekar Tambawal ba.

DUBA WANNAN: Sarkin Daura ya yaba da aikin Osinbajo

Sanata Wammakko ma dai cewa yayi gwamnan ya kwapsa, kuma abin tausayi ne, bayan da ya tara dubban magoya baya a rangadin sa na birnin Shehu.

Sai dai kuma, har yanzu, kar a manta, Tambawal, ya iya siyasar sa, wanda duk da ya sha sauya sheka, bai taba yo kasa ba a kujerun da yake hawa, inda har na hudu ya kai a kasar nan.

Gwamnan, ya kuma taba kwasar kujerarsa sukutum ta lamba hudu ya kaiwa APC, aka rasa yadda za'ayi dashi a wancan lokacin, kamar dai yadda Bukola Saraki yayi zarra a yau.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel