Murna da farin ciki a arewa yayin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki, hotuna

Murna da farin ciki a arewa yayin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki, hotuna

A ranar Talata, 26 ga watan Yuli na shekarar ne ministan aiyuka, lantarki da gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya kaddamar da fara aikin gyaran babbar hanyar da ta tashi daga Kano zuwa Abuja.

Masu amfanin da hanyar domin yin bulaguro sun dade suna korafi da yadda hanyar ta lalace har ta kai ga ana yawan samun yawaitar hatsarin mota a titin.

A shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar gyaran hanyar daga Abuja zuwa Kaduna bayan an rufe filin tashi da saukar jirage na Nmandi Azikiwe dake Abuja na tsawon sati biyu domin gudanar da wasu muhimman aiyuka.

Murna da farin ciki a arewa yayin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki, hotuna

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki

Murna da farin ciki a arewa yayin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki, hotuna

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki a arewa

Harkokin sufuri zasu inganta tare da rage yawaitar afkuwar hatsari idan aka kamala gyaran hanyar kamar yadda wasu mutane da suka halarci taron kaddamar da aikin suka fada cikin murna da farinciki.

DUBA WANNAN: Manyan aiyuka 6 da shugaba Buhari ya yi a kowanne yankin Najeriya

Sarkin Kano, Nuhammadu Sanusi II, manyan jam’ian gwamnatin tarayya, na jihar Kano, jama’ar gari da kuma ‘yan siyasa ne suka halarci wurin taron kaddamar da aiki.

Murna da farin ciki a arewa yayin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki, hotuna

Jama'a cikin murna da farin ciki yayin kaddamar da babban aikin gyaran titin Kano zuwa Abuja

Murna da farin ciki a arewa yayin da gwamnatin tarayya ta kaddamar da babban aiki, hotuna

Yayin kaddamar da babban aikin hanyar Kano zuwa Abuja

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel