Sarkin Daura yace Osinbajo na biyayya sosai ne ga Buhari a ziyarar da ya kai masa

Sarkin Daura yace Osinbajo na biyayya sosai ne ga Buhari a ziyarar da ya kai masa

- Ziyarar Osinbajo kauyen Daura bata kai ga an jefe shi ba

- Ba da dade wa ba ya sauke dan garinsu daga babban mukami

- Sarkin Daura ya yaba da irin aikin da Osinbajo keyi

Sarkin Daura yace Osinbajo na biyayya sosai ne ga Buhari a ziyarar da ya kai masa

Sarkin Daura yace Osinbajo na biyayya sosai ne ga Buhari a ziyarar da ya kai masa

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, ya tarbi shugaban kasa na wucin gadi, Farfesa Osinbajo, wanda ya sauke dan kauyen nasa daga babban mukami, Lawal Daura, inda yace duk ayyukan Osibanjon na kan daidai, kuma na taimakon gwamnatin Buhari.

A ziyarar da ya kai garin na Daura, saboda ya taya dan takarar jam'iyyarsa mai mulki APC, kamfe na zabukan maye gurbi da ake yi yanzu haka, ya yaba da aikin mukaddashin, inda yace ai shugaba Buhari yayi sa'ar mataimaki.

DUBA WANNAN: Sabbin hanyoyin shigo da man fetur arewa

Duk da ya sauke Lawal Daura, hakan bai hana cincirindon jama'a a garin ba zuwa tarbarsa.

Wannan na nufin wataki ko dai Lawal Daura bai gyara siyasar sa a garinsu ba, ko kuma mutan rin sun yi hangen nesa kan yadda dattijon ya fado babu nauyi.

Jama'a in bassu son mutum a arewa, ihu suke masa ko su jefe shi, amma ba'a yibwa Osinbajon haka ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel