Nigerian news All categories All tags
Tashin hankali: An samu biliyoyi, manyan bindigu da dubban katinan zabe a gidan Lawal Daura

Tashin hankali: An samu biliyoyi, manyan bindigu da dubban katinan zabe a gidan Lawal Daura

Rahoton da Newsbreakng ta wallafa a yau yace an gano makudden kudade har N21 biliyan a gidan tsohon shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS), Mallam Lawal Musa Daura dake babban birnin tarayya, Abuja.

Wata majiya dake da masaniya kan lamarin tayi ikirarin cewa an gano bindigogi sama da 4000 tare da wasu kananan makamai da kuma katin zabe mallakar wasu bakin haure daga jamhuriyar Nijar duk a gidan nasa.

Tashin hankali: An samu biliyoyi, manyan bindigu da dubban katinan zabe a gidan Lawal Daura

Tashin hankali: An samu biliyoyi, manyan bindigu da dubban katinan zabe a gidan Lawal Daura

Ana tuhumar tsohon shugaban DSS din ta karkatar da wasu makuden kudade $21 miliyan da ya gada daga tsohon shugaban hukumar DSS, Mr Ita Ekpenyong.

DUBA WANNAN: Canji: Ma’aikatar gwamnatin tarayya ta mayar da biliyan N3bn aljihun gwamnati

A halin yanzu Daura na amsa tambayoyi game da kudin pansho N12.9 biliyan da aka fitar daga asusun ajiya ta hukumar na DSS. Ana kuma tuhumarsa da hannu cikin cire N1.6 biliyan daga asusun ajiyar inshora na ma'aikatan hukumar, inji majiyar.

Sai dai babu wata kwakwarar majiya daga hukumar data tabbatar da afkuwar wannan lamarin saboda babu wanda yake son yin tsokaci kan babban batu irin wannan daya shafi tsohon shugaban hukumar ta DSS.

A ranar Alhamis data gabata, tsohon shugaban hukumar DSS, Ekpenyong ya bayyana a hedkwatan hukumar EFCC inda ya amsa tambayoyi kan yadda ya sarafa kudaden da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Kwanel Sambo Dasuki, ya bashi gabanin zaben shekarar 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel