Yanzu-yanzu: An harbe babban jigon jam'iyyar APC a jihar Ekiti har lahira

Yanzu-yanzu: An harbe babban jigon jam'iyyar APC a jihar Ekiti har lahira

Wasu yan bindiga sun harbe babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma hadimin tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar, Segun Oni, kwamred Bunmi Ojo, har lahira.

Majiya ya bayyana cewa an harbeshi ne a gidan kallon kwallo da yammacin Juma'a, 10 ga watan Agusta 2018, a babbar birnin jihar, Ado Ekiti.

Bumi Ojo ya kasance ma'aikacin hukumar tabbatar da adalcin daukan ma'aikatun gwamnati wato Federal Character Commission, ya tafi kallon kwallo ne da daren jiya a Opopogbooro amma bai dawo ba.

Yan bindigan sun bude masa wuta yayinda aka kammala wasan kwallon Manchester United da Leicester City misalin karfe 09:45 na dare.

Wadanda suka shaida abun sun bayyana cewa Bunmi Ojo a take ya mutu saboda irin harbin da suka masa. Wani mai jaje yace "babu wanda zai iya tsira a irin wannan harbi da akayi masa a kai."

Har yanzu dai bamu samu jawabi da gidan gwamnatin jihar ko hukumar yan sanda ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel