Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles mai suna Ahmad Musa ya bayyana matukar jin dadin sa da irin kyakkyawar tarbar da ya samu daga larabawan Saudiyya.

Idan ba'a manta ba fitaccen dan kwallon dai mai shekaru 25 a duniya ya sauya kungiyar kwallon sa ne ta Leicester City ya zuwa kungiyar kwallon Al-Nassr dake a kasar ta Saudiyya.

Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

Ahmad Musa ya samu kyakkyawar tarba daga larabawan kasar Saudiyya

KU KARANTA: Hotunan Nafisa Abdullahi da kowa ke magana

Legit.ng ta samu cewa sai da jim kadan da saukar sa a kasar ta Saudiyya ne sai kawai cincirindon masoya kwallo musamman ma na sabuwar kungiyar ta sa suka zagaye shi suna murnar komawar tasa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa fitaccen dan wasan tauraruwar sa ta haska sosai a gasar cin kofin duniya da ya gabata a kasar Rasha inda ya samu zura kwallaye biyu ringis a lokacin da Najeriya ta kara da kasar Iceland.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel