Da tsarin Doka ta Dimokuradiyya za a tsige Saraki - Oshiomhole

Da tsarin Doka ta Dimokuradiyya za a tsige Saraki - Oshiomhole

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana za ku ji cewa, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana yadda za a tsige shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ta hanya mafi dacewa ba tare da ta'addanci ba.

Shugaban jam'iyyar a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana cewa, jam'iyyar za ta bi tsaruka bisa tanadi irin dokar kasar da kuma dimokuradiyya wajen tsige shugaban majalisar ba tare da wani tashin hankali ba.

Oshiomhole yake cewa, turba daya ce Sarki zai hau mafi sauki domin gujewa tsige shi da mukamin sa wadda ba ta wuci ya yi murabus ba cikin lumana tare da samarwa kansa mutunci a idon al'ummar kasar nan.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana hakan da cewar Saraki bai ko dace da kujerar sa ba sakamakon mambobin majalisar mafi rinjaye dake jam'iyyar APC, saboda haka ba bu wata hanyar da 'yan tsirarun 'yan majalisar na jam'iyya maras rinjaye za su jagoranci mafi rinjaye.

Da tsarin Doka ta Dimokuradiyya za a tsige Saraki - Oshiomhole

Da tsarin Doka ta Dimokuradiyya za a tsige Saraki - Oshiomhole

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya bayyana hakan ne a shelkwatar jam'iyyar sa dake babban birnin kasar nan na Abuja, inda yake cewa Saraki ya ci amanar ta sakamakon babu wani hobbasa da ya yi bisa kujerar sa da manufa ta ci gaban kasa face soyuwa irin ta zuciyar sa.

KARANTA KUMA: Osinbajo zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata domin kaddamar da wasu ayyuka

Legit.ng ta fahimci cewa, ana ci gaba da wannan badakala tsakanin jam'iyyar APC da Saraki sakamakon sauyin shekar sa tare da Sanatoci da dama zuwa jam'iyyar adawa ta PDP, wadda a halin yanzu da yawa ke ganin bai cancanci ci gaba da rike mukamin sa ba.

A yayin hakan baya ga shan alwashi na tsige Saraki daga kujerar sa, Oshiomhole ya kuma bayyana cewa jam'iyyar za ta tabbata bai samu nasarar komawa majalisar dattawa ba a yayin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel