Yankan kauna: Budurwa 'yar shekara 17 ta yankewa saurayin ta azzakari a Jigawa

Yankan kauna: Budurwa 'yar shekara 17 ta yankewa saurayin ta azzakari a Jigawa

Wata budurwa mai shekaru akalla 17 a duniya da ta fito daga karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa mai suna Ramlatu Tafida a shiga kanun labarai bayan da ta sa wuka ta yanke azzakarin saurayin ta.

Kamar dai yadda muka samu, saurayin nata mai suna Abdullahi Sabo dake da shekaru 25 a duniya yanzu haka yana kwance a asibitin Malam Aminu Kano yan karbar kulawa.

Yankan kauna: Budurwa 'yar shekara 17 ta yankewa saurayin ta azzakari a Jigawa

Yankan kauna: Budurwa 'yar shekara 17 ta yankewa saurayin ta azzakari a Jigawa

KU KARANTA: Yan Kwankwasiyya sama da dubu dari 5 sun koma PDP a jihar Edo

Koda yake dai kawo yanzu ba mu samu wani cikakken bayani ba game da dalilin da yasa budurwar ta aikata hakan, amma dai mun samu cewa tuni har an makata kotu.

A wani labarin kuma, Jami'in dan sandan Najeriya a garin Abuja a ranar Juma'a ya gurfanar da wani mai sana'ar wanki da guga mai suna Benjamin Ayuba dake da shekaru 29 a duniya a gaban kuliya bisa zargin saida kayan jama'a da suka kawo masa wanki.

Dan sandan dai mai suna John Okpa da ya kai shi kara a kotun ya zarge shi ne da laifin zamba cikin aminci da kuma rashin gaskiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel