Sauyin sheka: Jama'a, fada fa ya kacame tsakanin Saraki da Adams Oshiomhole

Sauyin sheka: Jama'a, fada fa ya kacame tsakanin Saraki da Adams Oshiomhole

Shugaban majalisar dattijan Najeriya kuma jigo yanzu a jam'iyyar PDP Dakta Bukola Saraki aranar Juma'ar da ta gabata ya maidawa shugaban jam'iyyar APC, Kwamared Adams Oshiomhole martari game da kalaman da yayi a kansa.

Tun farko dai kamar yadda muka samu, Kwamared Adams Oshiombole ya kira taron manema labarai ne a ofishin sa dake a Sakatariyar jam'iyyar APC inda ya dage akan lallai sai an tsige Dakta Bukola Saraki daga mukamin sa na shugaban Majalisa.

Legit.ng ta samu cewa shi kuwa Saraki din a cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun sa ya fitar, ya mayarwa da Oshiomhole kakkausan martani inda ya kara jaddada cewa lallai ba zai ciru ba tare ma da kiran sa 'jahilin doka'.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu na nuna mana ne da cewa akalla wasu cincirindon mutane su 1,100 ne suka sanar da yanke hukuncin sauya shekar su daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP a karamar hukumar Etsako dake a jihar Edo.

Lokacin da yake karbar masu sauya shekar a hedikwatar jam'iyyar, shugaban jam'iyyar ta PDP a karamar hukumar mai suna Cif Dan Orbih ya yi maraba da su sannan kuma yayi masu alkawarin samun adalci mai dorewa a jam'iyyar.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel