Tsintisya ta watse: Wasu mutane 1,100 sun fice daga APC, sun koma PDP a jihar Edo

Tsintisya ta watse: Wasu mutane 1,100 sun fice daga APC, sun koma PDP a jihar Edo

Labarin da muke samu na nuna mana ne da cewa akalla wasu cincirindon mutane su 1,100 ne suka sanar da yanke hukuncin sauya shekar su daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP a karamar hukumar Etsako dake a jihar Edo.

Lokacin da yake karbar masu sauya shekar a hedikwatar jam'iyyar, shugaban jam'iyyar ta PDP a karamar hukumar mai suna Cif Dan Orbih ya yi maraba da su sannan kuma yayi masu alkawarin samun adalci mai dorewa a jam'iyyar.

Tsintisya ta watse: Wasu mutane 1,100 sun fice daga APC, sun koma PDP a jihar Edo

Tsintisya ta watse: Wasu mutane 1,100 sun fice daga APC, sun koma PDP a jihar Edo
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Tsohon gwamna a Arewa zai fice daga APC zuwa PDP

Legit.ng ta samu cewa wannan dai sauye-sauyen jam'iyyar da ake samu na zaman wata 'yar manuniya musamman ma ganin cewa shugaban jam'iyyar ta APC ya fito ne daga jihar ta Edo.

A wani labarin kuma, Shugaban majalisar dattijan Najeriya kuma jigo yanzu a jam'iyyar PDP Dakta Bukola Saraki aranar Juma'ar da ta gabata ya maidawa shugaban jam'iyyar APC, Kwamared Adams Oshiomhole martari game da kalaman da yayi a kansa.

Tun farko dai kamar yadda muka samu, Kwamared Adams Oshiombole ya kira taron manema labarai ne a ofishin sa dake a Sakatariyar jam'iyyar APC inda ya dage akan lallai sai an tsige Dakta Bukola Saraki daga mukamin sa na shugaban Majalisa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel