Fatanmu ace masu son mulkin kama karya sun gane kurensu - Saraki

Fatanmu ace masu son mulkin kama karya sun gane kurensu - Saraki

- Saraki ya gana da jam'iyun siyasa 45

- 7 ga watan Augusta ta zama rana mafi muni a garemu

- Bama goyan bayan duk wani abu na rashin Dimokradiyya

Fatanmu ace masu son mulkin kama karya sun gane kurensu - Saraki

Fatanmu ace masu son mulkin kama karya sun gane kurensu - Saraki

Saraki ya gana da jam'iyun siyasa 45 inda suka bayyana rashin jindadin su akan abinda ya faru a ranar Talata.

Yayin da suke ganawa da Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki a ranar Alhamis ciyaman na United Democratic Party da sakatare na CNN Godson Okeye yace "mun kawo wannan ziyara ne dan bayyana rashin jindadin mu akan abin daya faru a ranar Talata, 7 ga watan Augusta ta shiga cikin jerin munanan ranaku a garun wadanda basa son Damukradiyya da kuma makiyan Nageriya".

Wadannan jam'iyyu 45 sun samu jagorancin National chairman Chief Perry Opara wanda yayi magana da yawun su.

DUBA WANNAN: Kiwon Lafiya: Shawarar bankin duniya ga gwamnati

Yayin da yake magana Opara yace "Mambobin majalisa sune jarumai na kwarai a bangaren Dimokradiyya sannan a matsayin mu na shuwagabannin jam'iya bazamu zauna muna kallo kasarmu ta tabarbare ba."

Yayin da Saraki yake nuna farin cikin sa da wannan ziyara yace "Ina fata marasa goyan bayan Dimokradiyya sun gane kuskuran su a cikin kwanakin da suka gabata bayan sunji ra'ayin yan Nageriya, baya goyan bayan rashin Dimokradiyya da kuma rashin kundin tsarin mulki."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel