Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Kaduna ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Kaduna ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Da sanadin shafin jaridar The Cable mun samu rahoton cewa, mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Kaduna, John Kwaturu, ya sauya sheka daga jam'iyya mai ci ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Kwaturu ya shaidawa manema labarai cewa, tuni ya mika wasikar sa ta shiadar sa ta janye jiki daga jam'iyyar APC zuwa ga mazabar Kwaturu dake karkashin karamar hukumar Kachia ta jihar.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i

Ya ci gaba da cewa, ya zayyana dalilan barin jam'iyyar cikin rubutacciyar wasikar sa, ya kuma ce abin daɗaɗawa a halin yanzu shine shugaban mazabar Kwaturu kansa ya fice daga jam'iyyar ta APC.

Legit.ng ta fahimci cewa, Junaidu Yakubu, wani dan majalisa na mazabar Hunkuyi dake karamar hukumar Kudan ya fice daga jam'iyyar ta APC inda shima ya aika da wasikar sa zuwa ga shugaban mazabar tun a ranar 7 ga watan Agustan da ya gabata.

KARANTA KUMA: Jihar Gombe na fama da barazana ta hadarin cutar Kuturta

'Dan majalisar ya bayyana cewa, babban dalilin ficewar sa daga jam'iyyar bai wuci zalunci ta bangaren shugabannin jam'iyyar na kananan hukumomi da kuma na jihar baki daya.

A yayin haka kuma, wata majiyar rahoton ta bayyana cewa akwai 'yan majalisa 6 na jihar dake kan hanyar su ta ficewa daga jam'iyyar ta APC a mako mai gabatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel