Osinbajo zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata domin kaddamar da wasu ayyuka

Osinbajo zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata domin kaddamar da wasu ayyuka

A ranar Talata ta mako mai gabatowa, mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai kai ziyara jihar Zamfara dake Arewacin Najeriya domin kaddamar da wasu ayyukan gwamnatin jihar kamar Alhaji Lawan Liman ya bayyana., shugaban kwamitin cikar gwamnatin shekaru bakwai a kujerar mulki.

Liman ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata yayin da yake duban wasu ayyuka da mukaddashin shugaban kasar zai kaddamar a kananan hukumomin Talata-Marafa da kuma Bakura.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, bude wannan sabbin ayyuka yana daya daga cikin wani bangare na bukukuwan murnar cikar shekaru bakwai akan kujerar mulki na Gwamnan jihar, Abdulaziz Abubakar Yari.

Osinbajo zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata domin kaddamar da wasu ayyuka

Osinbajo zai ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata domin kaddamar da wasu ayyuka

Liman wanda kuma shine shugaban jam'iyyar APC na jihar ya bayyana cewa, ayyukan da za a kaddamar sun hadar da; Makarantar Mata da wata Babbar hanya gami da wata Firamare ta Abubakar Tinau a garin Mafara.

Sauran ayyukan sun hadar da; wata ma'aikatar ruwa garin Gamji da kuma babban asibitin garin Bakura da gwamnatin jihar ta sakewa fasali da kwaskwarima.

KARANTA KUMA: An yaudari wadanda suke tunanin Buhari na 'Yan Arewa ne kadai da Musulmai - Keyamo

A cewar sa, akwai kimanin ayyuka fiye da 100 da gwamnatin jihar ta kammala kuma ake sa ran kaddamar da su zuwa watan Nuwamba domin ci gaba da bukukuwa da murna a fadin jihar.

Liman ya kara da cewa, ana tsammanin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar ciki watan Satumba domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka na gwamnatin Yari.

Ya kuma nemi al'ummar yankin dake sharbar wannan romo da gwamnatin ta gyagije akan su ribaci amfanin sa ta hanyar kulawa da kuma tattali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel