Masu son ganin fadowar Saraki makiyan damokradiya ne – Gwamna Ortom

Masu son ganin fadowar Saraki makiyan damokradiya ne – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa wadanda ke hada makirci don ganin an tsige shugabannin majalisar dokoki na kasa sun kasance tamkar makiyan damokardiyyan Najeriya.

Gwamna Ortom ya bayyana haka ne a wani jawabi da aka aikawa Legit.ng a ranar Juma’a, 10 ga watan Agusta, yayinda jita-jita ke yaduwa na shirin tsige shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ekweremadu.

Gwamnan ya bukaci wadanda ke da hannu cikin shirin da su dubi kundin tsarin mulkin Najeriya tare da tsarin majalisar don fahimta.

Masu son ganin fadowar Saraki makiyan damokradiya ne – Gwamna Ortom

Masu son ganin fadowar Saraki makiyan damokradiya ne – Gwamna Ortom

Ya fahimci cewa ko da yake zaben shugaban majalisan dattawa yana bukatar masu rinjayi, haka kuma sauke mai rike da wannan mukamin kuma yana bukatar kaso biyu cikin uku na yan majalisan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dole a tsige Saraki - Oshimhole

Ya bayyana hari akan Saraki, tare da shirin tsige shi da kuma barazanar daskarar da asusun bankin shi a matsayin abin kaico da kuma Allah wadai.

Yace Saraki ya nuna da’a a shugabancin majalisar, tare da nuni ga cewa shugaban majalisar dattawan bai yi laifin komai ba wajen sauya sheka daga All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel