An yaudari wadanda suke tunanin Buhari na 'Yan Arewa ne kadai da Musulmai - Keyamo

An yaudari wadanda suke tunanin Buhari na 'Yan Arewa ne kadai da Musulmai - Keyamo

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito mun samu rahoton cewa, an yaudari wadanda su kayi tunanin shugaban kasa Muhammadu Buhari na 'yan Arewa kadai da Musulmai yayin babban zabe da ya gudana a shekarar 2015 da ta gabata.

Wani babban lauya kuma shugaban sadarwa na yakin neman zaben shugaba Buhari, Festus Keyamo, shine ya bayyana hakan a shafin sa na zauren sada zumunta.

Festus Keyamo

Festus Keyamo

Keyamo yake cewa, a halin yanzu ana sake yaudarar al'ummar Kirista na yankin Kudu dake laluben tsayar da dan takara Musulmi kuma dan Arewa a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Dogara da Kwankwaso sun yiwa Gwamna Dickson ta'aziyyar Mahaifiyar sa

Babban lauyan ya kuma bayyana cikin shafin na sa na sada zumunta cewa, sauyin shekar Sanata Akpabio daga jam'iyyar PDP zuwa APC ya dakusar da adawa ga musulmai 'yan arewa wadda jam'iyyar PDP ta dasa a zukatan al'ummar kudancin kasar nan tun a zaben 2015.

Ya kara da cewa, a halin yanzu anyi walkiya gaskiya ta bayyana dangane da yaudarar mutanen kasar nan ga kabila ko addinin dan takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel