Buhari fa ya dena cika bakin ba mai iya kada shi a 2019 - Babban aminin sa

Buhari fa ya dena cika bakin ba mai iya kada shi a 2019 - Babban aminin sa

Daya daga cikin dadaddun aminan shugaba Muhammadu Buhari da suka yi aiki tare a baya kuma tsohon ministan albarkatun man fetur na Najeriya Cif Tam David West ya gargadi aminin na sa da cewa ya fa dena tokobon cewa babu mai iya kada shi zabe a 2019.

Cif David ya kara da cewa duk da yake shi babban masoyin shugaban kasar ne kuma yana goyon bayan sake tsayawar sa takara a zaben mai zuwa, amma ya kamata ya fuskanci lamarin siyasar kasar da ido na basira.

Buhari fa ya dena cika bakin ba mai iya kada shi a 2019 - Babban aminin sa

Buhari fa ya dena cika bakin ba mai iya kada shi a 2019 - Babban aminin sa

KU KARANTA: Tsohon gwamna a Arewa ya kammala shirin komawa PDP

Legit.ng ta samu cewa ya kara da cewa dukkan masu fada masa cewar babu wanda zai iya kada shi zaben na 2019 mayaudara ne kuma ya kamata ya san cewa akwai tarin matsaloli sosai a kasar da ke bukatar agajin gaggawa.

A wani labarin kuma, Dubun dubatar al'umma masoya tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne suka sauya sheka ya zuwa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta jaridar Vanguard, 'yan kwankwasiyyar sun sauya shekar ne tare da wasu mambobin bangaren nan na 'yan awaren jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel