Kungiyar Kwankwasiyya a Filato sun kaddamar da goyon bayansu ga PDP

Kungiyar Kwankwasiyya a Filato sun kaddamar da goyon bayansu ga PDP

Mambobin kungiyar Kwanwasiyya a jihar Filato a rana juma’a sun doso sakateriyar jam’iyyar PDP a Jos inda suka bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar sannan kuma sun alwashin yin aiki don ganin PDP tayi nasara a zaben 2019.

Mambobi kungiyar wadanda suka kasance cikin shiga mai nuna alamar kwankwasiyya mai dauke da jan hula da farar riga sun samu jagorancin shugabankungiy na jihar, Tokji John.

John ya fadawa majiyarmu cewa, “mun ziyarci shugaban jam’iyyar na jiha, Hon. Damishi Sango don bayyana goyon bayanmu ga PDP a jihar Filato.

Kungiyar Kwankwasiyya a Filato sun kaddamar da goyon bayansu ga PDP

Kungiyar Kwankwasiyya a Filato sun kaddamar da goyon bayansu ga PDP

“Mun samu kyakkyawar tarba, mun kuma bada tabbacin zuwa kananan hukumomi don neman goyon baya saboda PDP ce zamu ba kuri’unmu.”

KU KARANTA KUMA: Zaben cike gurbi: An sanya dokar hana walwala a kananan hukumomi 7 a jihar Bauchi

Yace ya dauki kungiyan tsawon lokaci don bayyana goyon bayanta ga jam’iyyar PDP saboda yawancin mambobin majalisar zartarwa a jihar sun kasance mambobin APC, sannan kuma, sun bukaci neman shawarwari kafin yanke hukunci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel