Dogara da Kwankwaso sun yiwa Gwamna Dickson ta'aziyyar Mahaifiyar sa

Dogara da Kwankwaso sun yiwa Gwamna Dickson ta'aziyyar Mahaifiyar sa

Za ku ji cewa, kakakin majalisar wakilai Mista Yakubu Dogara, ya yiwa gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson ta'aziyyar mutuwar mahaifiyar sa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Marigayiyar Mrs Gold Coast Dickson, ta riga mu gidan gaskiya ne a da safiyar ranar Alhamis din da ta gabata a reshen cutar Daji na asibitin jami'ar Texas dake birnin Houston na kasar Amurka inda take jinya bayan ta sha fama da rashin lafiya.

Mista Dogara ya bayyana sakon ta'aziyyar sa ne ga gwamnan inda yake cewa wannan babban rashi na iyaye musamman uwa ba ya da misali ta fuskar ma'aunin halin da mutum yake shiga.

Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson

Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson

Legit.ng ta fahimci cewa, marigayiyar ta riga mu gidan gaskiya ne a yayin da take shekaru 72 a duniya inda ta sadaukar da rayuwar ta wajen jagoranci musamman ga al'ummar addinin ta na Kirisra.

KARANTA KUMA: Jihar Anambra ta fara cafke 'Yan Takara da ba su biyan Haraji

A wani rahoton na daban mun samu cewa, tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya aikawa da gwamnan na sa sakon ta'aziyyar a shafin sa na dandalin sada zumun ta na twitter.

Shugabannin biyu sun kuma yi addu'a tare da bayar da hakuri ga gwamnan, 'yan uwa, masoya da kuma abokanan arziki dangane da wannan babban rashi da ba bu mai maye gurbin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel