Bankin Duniya ga gwamnatin Najeriya: Ku sakar wa asibitoci kudi don talakawa su sami kulawa

Bankin Duniya ga gwamnatin Najeriya: Ku sakar wa asibitoci kudi don talakawa su sami kulawa

- Domin Najeriya ta fita daga halin tabarbarewar cibiyoyin lafiya, dole ta watsa kayayyakin aiki ta hanyar Performance Based Financing (PBF)

- Najeriya ta tabbatar da tana bibiyar yanda ake amfani da kudaden BHCPF da kuma nasarorin da ake samu

- Bada kyauta ga jihohi da suka habaka a fannin kiwon lafiya hanyace ta karfafa su

Bankin Duniya ga gwamnatin Najeriya: Ku sakar wa asibitoci kudi don talakawa su sami kulawa

Bankin Duniya ga gwamnatin Najeriya: Ku sakar wa asibitoci kudi don talakawa su sami kulawa

Kungiya bankin duniya tayi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta yada kudin ababen da ake bukata na cibiyoyin kiwon lafiya. Sannan kuma a samar da tsarin aiki ga ma'aikatan.

A rana uku ta THISDAY Healthcare Policy Dialogue da akayi kwanan nan a Abuja, shugaban Nutrition da Population na kungiyar bankin duniya dake Washington DC, Benjamin Loevinsohn, ya bayyana cewa, Idan ana so Najeriya ta fita daga halin tabarbarewar cibiyoyin lafiya da take fama dashi, dole ne ta saki kudin kudin kayan aiki tare da aiki ta Performance Based Financing (PBF).

A gabatarwa da yayi akan 'Achieving UHC in Nigeria - How to Support States', yace "Najeriya ta tabbatar da Basic Health care provisions Fund, tare da bibiyar yanda ake amfani da kudaden da kuma nasarorin da aka samu bayan an amfana. Ta haka ne kawai zamu cimma manufar mu."

Yace kyautatawa jihohin da suka samu cigaba ta ingancin kiwon lafiya ma zai taka rawar gani wurin habakawar.

DUBA WANNAN: Martanin Lawal Daura

Yace :"Shirin Saving One Million Lives Performance for Reward wani makami ne na gyara matsalolin cibiyoyin kiwon lafiya a kasar nan. Idan ana kyautatawa jihohi zasu dage gurin ganin suna aiki fiye da da."

Yace ana amfani da Smart Survey ne gurin gwajin aikin, wanda United Nations Children’s Fund da NBS suke shiryawa.

Ana kirga jimillar rigakafi, sinadarin Vitamin A, gidan sauro, kwararrun masu karbar haihuwa, duba cutar HIV lokacin awon ciki da dai sauran su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel