Gwamna El-Rufai ya ba wani Saurayi matsayi a Gwamnatin sa

Gwamna El-Rufai ya ba wani Saurayi matsayi a Gwamnatin sa

Mun samu labari cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna ya nada wani Bawan Allah Matashi mai suna Injiniya Muhammed Maccido Usman a cikin Gwamnatin sa kwanan nan. Maccido kwararren Injiniya ne a harkar man fetur.

Gwamna El-Rufai ya ba wani Saurayi matsayi a Gwamnatin sa

El-Rufai ya nada wani Matashi a cikin Gwamnatin Kaduna

A makon nan ne Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya nada Muhammed Maccido Usman a matsayin daya daga cikin masu ba sa shawar. Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna Balarabe Abbas Lawal ne ya tabbatar da wannan.

Sakataren Gwamnatin Jihar ya aikawa wannan Matashi takarda inda aka bayyana masa cewa an nada shi a matsayin Hadimin Gwamnan Jihar wanda ofishin sa ya fara aiki a Ranar Laraba watau 8 ga wannan Watan na Agusta.

KU KARANTA: An yi wa Kwankwaso ihun Sai Buhari a wajen sallar Juma'a

Gwamnan ya nada Maccido Usman ne bayan la’akari da dinbin basirar sa da sanin aiki da cigaban al’umma. Kafin nan dama Injiniya Maccido Usman da wasu Matasa da dama sun yi wani aiki da Gwamnatin ta Jihar Kaduna.

A takardar nadin mukamin an nemi wannan matashi ya soma aiki nan da makonni biyu. Muhammed Maccido Usman yayi karatu ne a Jami’ar Imperial college ta Landan inda ya zama Zakara lokacin da yayi Digir-gir a harkar fetur.

Dama kun ji cewa wasu Masu ba Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje shawara sama da 10 sun bi sahun tsohon Mataimakin Gwamna sun yi murabus su ma duk a makon nan bayan ficewar Kwankwaso daga Jam'iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel