Wike ya bukaci Osinbajo da ya sallami shugaban EFCC

Wike ya bukaci Osinbajo da ya sallami shugaban EFCC

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bukaci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya tsige shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, bisa daskarar da asusun bankunan gwamnatocin jihar Benue da Akwa Ibom da yayi.

Gwamnotocin biyu sun bayyana hakane kwana uku da suka gabata kan daskarar da asusun bankunansu, wanda hakan yayi sanadiyan gurgunce ayyukan gwamnati.

Hukumar ta janye iyaka da ta sanya wa asusun bankunan ne bayan al’uman Najeriya sunyi Allah wadai da aikin EFCC.

Mista Wike yace idan har za’a iya tsige shugaban hukumar DSr saboda tsare majalisan dokoki na kasa, shugaban EFCC ma ya cancanci a gurfanar da shi bisa aikin daukaka kan jihohin biyu.

Wike ya bukaci Osinbajo da ya sallami shugaban EFCC

Wike ya bukaci Osinbajo da ya sallami shugaban EFCC

Mista Wike yace hukumar EFCC, a matsayin hukuma dake karkashin jagorancin gwamnatin tarayyar APC, ta bi gwamnatin jihar Benue ne saboda sauya sheka da gwamna Samuel Ortom yayi, daga APC zuwa PDP.

Gwamnan ya alakanta matakin hukumar a Akwa Ibom ga sauya shekar tsohon shugaban yan PDP a majalisar dattawa, Godswill Akpabio daga PDP zuwa APC.

KU KARANTA KUMA: Ministan lafiya ya je garin Yola don ganin Duduwale mutumin da ya je Abuja da kafa don rantsar da Buhari (hotuna)

Yace hukumar EFCC na yiwa gwamnatin jihar Rivers bita da kulli.

Ya yi kira ga kungiyar gwamnonin Najeriya da su kare yancin jihohi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel