A karon farko: Lawal Daura ya bada dalilin da yasa yayi kokarin mamaye majalisa a makon nan

A karon farko: Lawal Daura ya bada dalilin da yasa yayi kokarin mamaye majalisa a makon nan

- "Na tura jami'ai ne saboda na samu labarin wasu mutane suna shirin shigar da makamai da wasu abubuwan ta'addanci majalisar"

- Jami'an yan sandan farin kaya sun mamaye kofar shiga zauren majalisar dattawa a ranar talata

- Boma Goodhead, yar majalisar wakilai daga jihar Rivers (PDP) ta tunkari jami'an

A karon farko: Lawal Daura ya bada dalilin da yasa yayi kokarin mamaye majalisa a makon nan

A karon farko: Lawal Daura ya bada dalilin da yasa yayi kokarin mamaye majalisa a makon nan

Korarren Darakta Janar na DSS, Lawal Musa Daura, ya bayyana cewa ya tura jami'an ne saboda labarin da yazo mishi na cewa ana shirin shigar da muggan makamai da wasu ababen ta'addanci majalisar.

Ya bayyana hakan ne a rahoton bincike da Sifeto Janar na 'yan sanda, Idris Ibrahim ya kai wa mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

A wani rahoton da majiyar mu ta samu, IGP Idris yace Daura ya hana shiga majalisar dattawa ba tare da yardar mukaddashin shugaban kasar ba.

"Tsohon shugaban yan sandan farin kaya, Mista Lawal Daura, yayi aikin gaban kanshi ba tare da ya sanar da shugabancin kasar ba. Bai sanar da kowa ba ko wata cibiyar tsaro akan hakan," inji rahoton Idris.

DUBA WANNAN: Gwamnonin Ibo zasu zo APC

Idris yace dalilan da Daura ya bada basu gamsar ba tunda babu jami'an Explosive Ordinance Disposal ko wasu kwararrun a gurin.

Boma Goodhead, yar majalisar wakilai, mai wakiltar jihar Rivers(PDP) ta tunkari jami'an da cewa Idan sun isa su harbeta.

Mukaddashin shugaban kasar,wanda ya kori Daura akan hana shiga zauren majalisar da aka wa mahukuntan, yace abinda Dauran yayi yaci Karo da kundin tsarin mulki da kuma dokar kasar.

Shuwagabannin majalisar dattawa da ta wakilai sun yi ala wadai da hakan domin sunce "Wannan juyin mulkin damokaradiyya ne".

Amma kuma APC sun jinjiinawa hana shiga majalisar domin hakan ya datse hargagi da hayaniyar da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki zai iya kawowa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel