Wani ‘Dan Majalisar APC ya bayyana abin da ya wakana ranar da DSS su ka yi wa Majalisa zobe

Wani ‘Dan Majalisar APC ya bayyana abin da ya wakana ranar da DSS su ka yi wa Majalisa zobe

Wani ‘Dan Majalisan Jam’iyyar PDP daga Yankin Jihar Edo Honarabul Ehiozuwa Agbonayinma ya zargi ‘Yan uwan sa da kokarin ganin bayan sa inda yace sun aika masa da tsageru su ka hana sa shigowa cikin Majalisar.

Wani ‘Dan Majalisar APC ya bayyana abin da ya wakana ranar da DSS su ka yi wa Majalisa zobe

Hon. Agbonayinma ya zargi PDP da shigo da ‘Yan daba cikin Majalisa

Ehiozuwa Agbonayinma da ke wakiltar wani bangare na Jihar Edo a Majalisar Wakilan Tarayyar kasar nan ya bayyana cewa Abokan aikin sa da ke karkashin Jam’iyyar PDP sun yi kokarin ci masa mutunci a Ranar Talatar nan da ka yi rikici a Majalisa.

Hon. Ehiozuwa Agbonayinma yana cikin ‘Yan Majalisar APC da su ka shigo Majalisa a ranar da Jami’an tsaro na DSS su ka zagaye harabar Majalisar kasar. ‘Dan Majalisar na Edo yace ‘Yan PDP ne su ka aiko ‘Yan daba su sare sa lokacin da ya hallara.

KU KARANTA: An ga ‘Yan Majalisa da kayan barasa bayan takaddamar DSS

Honarabul Agbonayinma ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa Takwarorin sa irin Matthew Uroghide da Sanata Dino Melaye ne su ka cece sa a ranar Talata har ya iya shiga Majalisar a lokacin da sauran abokan aikin sa da ke PDP su ka hana sa shigowa.

‘Dan Majalisar yace ‘yan daban da aka kawo sun yi kokari su ka hana kowa shiga Majalisar illa ‘Yan Jam’iyyar PDP face da aka samu taimakon DSS. A dalilin haka ne ‘Dan Majalisar na APC yake ganin babu wadanda su ka kitsa wannan danyen aiki sai PDP.

A makon nan ne Jami’an DSS su ka yi kokarin hana ‘Yan Majalisar shiga ofisoshin su wanda har ta kai Mukaddashin Shugaban Kasa yayi wuf tsige Shugaban DSS na kasa Lawal Daura don haka ‘Dan Majalisar yayi kira a binciki wannan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel