Idan har ba ayi maganin barayin dukiyar Gwamnati ba; Najeriya ba za tayi kyau ba – Ribadu

Idan har ba ayi maganin barayin dukiyar Gwamnati ba; Najeriya ba za tayi kyau ba – Ribadu

Shugaban Hukumar EFCC na farko da aka yi a tarihi, Nuhu Ribadu ya nemi a yaki rashin gaskiya a Najeriya. Ribadu yace idan har ana so ‘yan gaba su ji dadin kasar nan dole sai an tashi tsaye an yi wannan aiki.

Idan har ba ayi maganin barayin dukiyar Gwamnati ba; Najeriya ba za tayi kyau ba – Ribadu

Nuhu Ribadu yace barayin kasar nan su ka jawo duk wata matsala

Tsohon Shugaban EFCC Nuhu Ribadu yayi hira da Jaridar nan ta The Cable a jiya Alhamis inda ya bayyana cewa dole a fito a yaki rashin gaskiya da barna domin a bar wa mutanen da za a haifa nan gaba a Najeriya kasar da za su ji dadin zama.

Ribadu ya nemi a samu hadin-kai da yadda da juna tsakanin Gwamnati da kuma Talakawa wajen yakar masu barna da dukiyar jama’a. Ribadu da yake jawabi a Abuja yace dole sai jama’an kasa sun dage domin a ceci Najeriya don gaba.

KU KARANTA: Jama'a sun koka game da yadda masu wuta ke tatsar su

Idan har ba a fito an yi da rashin gaskiya ba, tsohon Shugaban Hukumar mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, yana ganin babu inda za a je a kasar. Ribadu yace satar dukiyar Talakawa da ake yi ne uwar fitinar duk barnar da ake gani.

Ribadu yace masu satar dukiyar kasa su ka jefa kasar nan cikin halin rikici da rashin tsaro da ake ciki. Nuhu Ribadu yace satar kudin tsaro ya ja aka yi shekara da shekaru ana fama da Boko Haram. Ribadu yace a wasu kasashe ba haka abin yake ba.

Yanzu haka ma dai kun ji cewa bisa dukkan alamu abubuwan ba su tafiya daidai tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya na ASUU bayan da Kungiyar tayi barazanar za za ta sake shiga yajin aiki kwanan nan idan aka yi sake.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel