Sojoji sun kashe mutane 7 sannan sun dakile harin Boko Haram

Sojoji sun kashe mutane 7 sannan sun dakile harin Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta kashe yan ta’addan Boko Haram bakwai a wani hari da tayi nasarar dakilewa a Gundari, karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno.

Dakarun sojin sun gudanar da aikin ne a ranar Alhamis a kokarinta na maida martani ga harin da yan Boko Haram suka kai sansanin sojin.

Sojin sun kuma illata yan ta’adda da dama a harin, Kanal Onyeama Nwachukwu, mataimakin daraktan kakakin rundunar sojin Operation Lafiya Dole ya sanar da hakan.

Sojoji sun kashe mutane 7 sannan sun dakile harin Boko Haram

Sojoji sun kashe mutane 7 sannan sun dakile harin Boko Haram

Rahotanni da ake kawo a baya sun nuna cewa yan ta’addan dauke da mugga makamai sun kai harin bazata sansanin soji a yankin ara ranar 6 ga watan Agusta.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar arewa na so Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa, sun bukaci Oshiomhole ya tabbatar da tsige Saraki

Nwachukwu yayi bayanin cewa dakarun sun yi nasarar dakile harin inda suka kashe yan ta’adda bakwai yayinda da dama suka tsere da raunuka.

Ya kuma bayyana cewa sojoji takwas sun ji rauni a harin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel