2019: Shugaban kasa Buhari ya ba Ministar sa da ke neman Gwamna tabarruki

2019: Shugaban kasa Buhari ya ba Ministar sa da ke neman Gwamna tabarruki

Ministar harkokin mata da walwalar al’umma Sanata Aisha Jummai Alhassan ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana goyon bayan takarar Gwamnan da ke shirin yi a zaben 2019.

2019: Shugaban kasa Buhari ya ba Ministar sa da ke neman Gwamna tabarruki

Ministar harkokin mata da Aisha Jummai Alhassan tace mata sun fi maza amana

Aisha Alhassan za ta fito takarar kujerar Gwamna a Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC mai mulkin kasar. a zaben 2019. Ministar tace Shugaban kasa Buhari da kan sa ya tofa mata albarka a zaben da za ayi kamar yadda ta bayyana jiya a Legas.

KU KARANTA: Wasu matan Najeriya na makale a Kasar Saudiyya har gobe

Ministar matan ta yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da Ma’aikatar mata ta shirya domin kawar da talauci. Alhassan ta tabattar da cewa za ta sake neman takarar Gwamna a zaben 2019. Sanata Alhassan tace su mata sun fi maza amana.

Sanata Alhassan ta nuna cewa babu abin da za a ji wa tsoro ko ta karaya wajen takarar inda ta nemi ‘Yan uwan ta su fita ayi da su a Gwamnatin ganin cewa Shugaba Buhari yayi alkawarin gudanar da zabe na gari mai cike da inganci a shekarar 2019.

Alhassan wanda ta na cikin Ministocin Gwamnatin Buhari ta na neman sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar Taraba a zabe mai zuwa da za ayi a 2019. Kwanan nan ne wani Ministan Kasar watau Kayode Fayemi ya lashe zaben Gwamnan a Ekiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel