Kungiyar arewa na so Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa, sun bukaci Oshiomhole ya tabbatar da tsige Saraki

Kungiyar arewa na so Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa, sun bukaci Oshiomhole ya tabbatar da tsige Saraki

Wata kungiyar arewa karkashin jagorancin Arewa Solidarity Front (ASF), ta bukaci shugaban jan’iyyar APC, Adams Oshiomhole day a tabbatar da cewa an tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki daga kan kujerarsa sannan kuma a maye gurbinsa da shugaban yan tsiraru a majalisa, Godswill Akpabio.

Kungiyaar ta bayyana cewa zasu samu goyon bayan sanatocin arewa domin tabbatar da ganin cewa Akpabio ya yi nasara, sun kara da cewa sun kammala shirye shirye domin samar da akalla sa hannu miliyan biyu domin yin waje da Saraki.

Kungiyar arewa na so Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa, sun bukaci Oshiomhole ya tabbatar da tsige Saraki

Kungiyar arewa na so Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa, sun bukaci Oshiomhole ya tabbatar da tsige Saraki

A wata wasika da aka gabatar ga Oshiomhole ta hannun sakataren APC a jihar Kaduna, Mohammed Bello Shuaibu, shugaban ASF, Haruna Abdullahi Maikano sun ce: “A matsayin kungiyar aewa mai kula da cigaban damokradiya, bazamu iya nade hannu mu kalli masu son zuciya dake kokarin gurgunta damokradiya da kuma illata ra’ayin jama’a.

KU KARANTA KUMA: 2019: Bafarawa yayi alkawarin yin biyayya ga PDP

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa a karshen makon nan ne Hukumar INEC za ta gudanar da zaben Sanata na Yankin Arewacin Katsina inda za a buga takara tsakanin wasu manyan ‘Yan siyasa da su ka fito daga gida guda a cikin Jihar ta Katsina.

Ko dai ya ta fadi sha ne ga ‘Yan gidan Babba Kaita a Katsina inda Yaran gidan 2 za su yi takara da juna a zaben Sanatan Yankin Daura a PDP da APC. Honarabul Ahmad Babba Kaita ne zai buga da ‘Dan uwan sa na jini watau Kabir Babba Kaita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel