Dan shekara 42 ya lalata ýar makwabcinsa mai shekara 11

Dan shekara 42 ya lalata ýar makwabcinsa mai shekara 11

Wata kotun majistare dake Ikeja ta gurfanar da wani mai aikin gini dan shekara 42 , Isaac Yakubu a kurkukun Kirikiri kan zargin lalata yarinyar makwabcinsa yar shekara 11 a duniya.

Alkalin kotun P. E. Nwaka yace a cigaba da tsare Yakubu har zuwa lokacin da zai ji shawarar da daraktan sashin hukunta jama’a zain yanke.

Yakubu, wadda ke zama a gida mai lamba 4, unguwar Mustapha Adeleke, Abule-Odu, Egbeda, ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Yuli a gidansa.

Jami’in dan sanda mai kara Christopher John yace mai laifin ta batar da kudin da aka aike ta.

Dan shekara 42 ya lalata ýar makwabcinsa mai shekara 11

Dan shekara 42 ya lalata ýar makwabcinsa mai shekara 11

"Lokacin da yayinyar ke kuka zuwa gida, wanda ake zargi wadda a gida daya suke, ya batra N200 sannan ya lalata ta a wani kangon gini.

“Yarinyar ta je gida da kuka inda ta fadawa mahaifiyarta abunda ya faru.

KU KARANTA KUMA: Ba zan nemi takarar ko wani kujerar siyasa a 2019 ba – Lai Mohammed

“An kai karar lamarin ofishin yan sanda sannan aka kama wanda ake zargin,” ya fadama kotu.

Za’a ci gaba da sauraron karar a ranar 9 ga watan Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel