2019: Bafarawa yayi alkawarin yin biyayya ga PDP

2019: Bafarawa yayi alkawarin yin biyayya ga PDP

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa zai cigaba da kasancewa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) koda kuwa ace ba’a bashi tikitin takarar jam’iyyar ba a zaben shugaban kasa na 2019.

Bafarawa wadda ke neman takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja a jiya.

Yayi Magana akan yiwuwar tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki kafin ya kai karshen wa’adin shugabancinsa a 2019, cewa ya zama dole a girmama dokar gwamnati mai inganci da kuma jam’iyya a koda yaushe.

2019: Bafarawa yayi alkawarin yin biyayya ga PDP

2019: Bafarawa yayi alkawarin yin biyayya ga PDP
Source: Depositphotos

Bafarawa yace yana maraba da samun sabbin yan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP.

KU KARANTA KUMA: Ba zan nemi takarar ko wani kujerar siyasa a 2019 ba – Lai Mohammed

Ya soki tsoffin gwamnoni dake mulki a matsayin sanatoci a majalisar dokokin kasar. A cewarsa wasu daga cikin tsoffin gwamnonin sun maida majalisar dokokin kasar wajen boyewa domin guje ma tozarci akan abubuwan da suka aikata a lokacin da suke kan mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel