Ana jiran tsammanin wasu gwamnonin jihohin kabilar Igbo zuwa APC 'kwanan nan'

Ana jiran tsammanin wasu gwamnonin jihohin kabilar Igbo zuwa APC 'kwanan nan'

- Gwamnonin biyu na kudu maso gabas zasu koma jam'iyyar APC nan ba da dadewa ba

- Wannan labari ne mai dadi garemu da kuma makomar gwamnonin

- Kada yan Najeriya suga canjin jam'iyyar a matsayin kiyayya, sai dai ra'ayi kawai na siyasa

Ana jiran tsammanin wasu gwamnonin jihohin kabilar Igbo zuwa APC 'kwanan nan'

Ana jiran tsammanin wasu gwamnonin jihohin kabilar Igbo zuwa APC 'kwanan nan'

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana cewa gwamnoni biyu daga kudu maso yamma zasu canza sheka zuwa jam'iyyar APC, ba tare da ya fadi sunayen su ba.

A jiya ne da yayi magana da manema labarai, a wata tataunawar kafafen yada labarai a Owerri, gwamnan yacey: "Wannan labari ne mai dadi garemu da kuma makomar mu cewa gwamnoni biyu na kudu maso gabas zasu tsallake, su shiga jirgin chanji kafin zaben 2019."

Okorocha yace canjin jam'iyya daga APC zuwa PDP da wasu sukayi ya faru ne tun shekaru biyu da suka gabata amma sai yanzu suka nuna, kari da cewa ra'ayin siyasa ne suka sa canjin shekar.

Ya sanar da yan Najeriya da kada su duba canjin jam'iyyar a wani abu face wani ra'ayi na yan siyasar.

Maganganun shi: "APC bata cikin rudani saboda wasu sun bar jam'iyyar. APC tana nan lafiya kuma da hadin kai. Muna girmama shugaban kasar saboda mun yarda da mulkin shi. Har yanzu Muhammadu Buhari ne gwanin mu. Har kuma 2019."

Ya kara da cewa inyamurai ma su kara rubuta tarihin siyasar su kuma su canza zancen su a zaben 2019, duk da ina farinciki cewa inyamurai sun koma yanda suke a da kuma sun shirya yin siyasar su ta gaskiya ta hanyar ba wa shugaba Buhari kuri'un su daga kudu maso yamma.

Ya kara da cewa, "A zaben da ya gabata, PDP ta kawo bambamcin addini da yare a kudu maso gabas. Yanzu kuwa kanmu ya waye."

DUBA WANNAN: 'NEPA na kuntata wa talakawa'

Gwamnan ya sanar da 14 da 15 ga watan Augusta su zamo ranakun hutu domin yan jihar su samu yin katin zabe na dindindin, kari da cewa kasuwanni da shaguna su zamo a rufe har sai karfe 4 na yamma.

Gwamnan yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar na kwana uku don kaddamar da wasu aiyuka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel