Ba zan nemi takarar kowani kujerar siyasa ba a 2019 – Lai Mohammed

Ba zan nemi takarar kowani kujerar siyasa ba a 2019 – Lai Mohammed

Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kwara kuma ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa ba zai yi takarar kowani kujerar siyasa a zaben 2019 ba.

Ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su canja fafutukar son zuciyarsu zuwa hadin kai.

Ba zan nemi takarar kowani kujerar siyasa ba a 2019 – Lai Mohammed

Ba zan nemi takarar kowani kujerar siyasa ba a 2019 – Lai Mohammed
Source: UGC

Da yake Magana a taron siyasa da jam’iyyar ta shirya a Ilorin a ranar Alhamis, Alhaji Lai Mohammed ya umurci mutanen jihar da su dauki makomarsu a hannunsu sannan su kwato abunda yake mallakarsu ne.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan fashi sun kashe mutane 10, sannan sun sanyawa motar kwamanda wuta a harin bankunan Edo

Sauran mutanen da suka yi Magana a taron baya ga Lai Mohammed sun yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su dauki matakin hana rabuwar kai da kuma tashin hankula da kan faru wajen zaben fid da gwani sannan su jajirce don ganin sun yi nasara a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel