Jihar Anambra ta fara cafke 'Yan Takara da ba su biyan Haraji

Jihar Anambra ta fara cafke 'Yan Takara da ba su biyan Haraji

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Anambra karkashin jagorancin gwamna Willie Obiano, za ta fara dakumar 'yan takarar kujerun siyasa cikin jihar dake kauracewa biyar haraji da ya rataya a wuyan su.

Shugaban hukumar kula da tallace-tallace na jihar, Mr Jude Emecheta, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema cikin farfajiyar ofishin sa a ranar Alhamis din da ta gabata.

Yake cewa, gwamnatin jihar na bukatar 'yan takara masu tallata kawunan su da biyan haraji sakamakon sanya hotuna jikin motocin yakin neman zabe gami da manne-mannen fastocin su.

Gwamnan Jihar Anambra - Willie Obiano

Gwamnan Jihar Anambra - Willie Obiano

Ya ci gaba da cewa, wannan shiri da gwamnatin jihar ta dabbaka ba ya nufin farautar kowace jam'iyya cikin jihar sabanin yadda ake yada jita-jita da kazafi wanda hakan ya tabbatar da rashin adalci ga gwamnatin jihar.

Ya yi watsi da da'awar cewa, gwamnatin na yunkurin fifita jam'iyyar mai ci a jihar ta APGA wajen fifita sama da sauran jam'iyyu a yayin da zaben 2019 ke ci gaba da karatowa.

KARANTA KUMA: 'Yan Boko Haram sun kai hari Sansanin Dakarun Soji, sun kar Dakaru 17 sun raunata 14 a jihar Borno

Emecheta ya kara da cewa, tuni hukumar ta kammala shirye-shiryen ta na cafke duk wani dan siyasa tare da dukumar motoci da hotunan 'yan siyasa suka bayyana a jiki ba tare da biya ma su haraji.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar ta na yiwa wannan lamari na 'yan siyasar a matsayin wani nau'i na tallace-tallace da yake bukatar sauke nauyin haraji da rataya a bisa tsari da kuma doka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel