Babban sufetan Yansanda ya bayyana abubuwa 10 da suka bankado a yayin bincikar Lawal Daura

Babban sufetan Yansanda ya bayyana abubuwa 10 da suka bankado a yayin bincikar Lawal Daura

A ranar Alhamis, 9 ga watan Agusta ne babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun ya mika ma mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo rahoton binciken da ya umarci hukumar Yansanda ta yi game da bahallatsar tsohon shugaban DSS, Lawal Daura.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a cikin wasikar, Idris ya shaida ma Osinbajo sunan wani kwararren jami’in Dansanda mai mukamin kwamishina,Garba Baba Umar ne ya gudanar da bincike akan Lawal Daura a wani gida dake Kebbi Close a unguwar Garki Crescent II Abuja, kuma ya gano muhimman bayanai, kamar haka:

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ye nemi izinin yin binciken kwakwaf akan Lawal Daura

- A ranar 7/8/2018 jami’an DSS sun far ma majalisar dokokin Najeriya akan umarnin Lawal Daura

- Jami’an DSS sun hana yan majalisu da ma’aikatan majalisar shiga majalisar

- Bincike ya tabbatar jami’an hukumar DSS ne suka hana yan majalisar shigar majalisa

- Wasu daga cikin jami’an sun rufe fuskokinsu

- Kafatanin jami’an na dauke da bindigu, kuma sun mamaye majalisar

- Jami’an sun wulakanta yan majalisar tare da cin mutuncinsu da kum yi ma rayuwarsu barazana

- Jami’an DSS sun gudanar da aiki kamar Sojojin haya da zasu aikata wani mugun aiki

- Lawal Daura ya yi gaban kansa ba tare da neman izinin fadar shugaban kasa ba

- Lawal Daura bai bayyana ma saura hukumomin tsaro ba, kuma ba basu bayanai ba

- Batun wai hukumar DSS ta samu wani bayanan sirri ne ba gaskiya bane, tunda jami’an da ta tura ba masu kwance ababen fashewa bane.

Babban sufetan Yansanda ya bayyana abubuwa 10 da suka bankado a yayin bincikar Lawal Daura

Lawal Daura

Hakazalika rahoton ya shawarci mukaddashin shugaban kasa tare da bukatar hadin kansa akan abubuwa guda uku da suka hada:

- A mika ma hukumar Yansanda dukkanin jami’an da suka yi wannan aiki a ranar 7/9/2018

- Akwai bukatar hukumar Yansanda ta binciki gidan Lawal Daura da na dukkanin jami’an da suka yi wannan aiki

- A mika mata wayoyi da kwamfutocin Lawal Daura da na sauran jami’an da suka yi wannan aiki don bincikensu.

Daga karshe babban sufetan Yansanda ya tabbatar ma Osinbajo cewa bayanan da Lawal Daura sun nuna akwai wasu manyan yan siyasa dake biyansa don biyan bukatunsu na kashin kai, kuma su yake yi ma aiki

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel